logo

HAUSA

Yadda kasashen Sin da Afirka ke yin hadin gwiwa wajen neman ci gaba tare

2024-07-10 11:03:16 CMG Hausa

A cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar Sin ta zama babbar abokiyar hadin gwiwar Afirka musamman a fannin cinikayya. Kuma Kusan kashi 20 cikin 100 na kayayyakin da yankin ke fitarwa a yanzu yana zuwa ne daga kasar Sin yayin da kusan kashi 16% na kayayyakin da ake shigowa da su Afirka na zuwa ne daga kasar Sin, a cewar asusun lamuni na duniya wato IMF. Darajar wannan hadakar ta kai dalar Amurka biliyan 282 a jimlar yawan cinikayya tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2023. Kayayyaki kamar karafa, da albarkatun ma'adinai da man fetur na wakiltar kashi uku bisa biyar na kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa kasar Sin, yayin da ta kan shigo da kayayyakin da Sin ke kerawa, kamar na'urorin lanturoni da injina da dai sauransu.

Haka kuma, jarin kai tsaye na kasar Sin wato FDI ya karu sosai cikin shekaru ashirin da suka gabata. Alal misali a shekara ta 2003, yawan jarin kai tsaye na shekara-shekara da kasar Sin ta zuba a Afirka ya kai kusan dala miliyan 75. Yayin da adadin ya cilla sama zuwa dala biliyan 5 a shekarar 2022. Shirin shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)”, ya kasance dabarun bunkasa duniya da aka kaddamar a shekarar 2013, wanda a karkashinsa ne ake gudanar da tsarin zuba jari kai tsaye na kasar Sin da nufin bunkasa harkokin sufuri, makamashi da ma'adinai. Haka ma shirin FOCAC na taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da hadin gwiwar bangarorin biyu gaba.  Shugabannin kasashen Afirka da al’ummar nahiyar Afirka sun yaba da wannan hadin gwiwa ta neman ci gaba tare tsakanin Sin da nahiyar. 

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a taron tsaro da aka gudanar a  Munich a watan Fabrairun bana ya ce, "Idan ba ka kan teburin abinci a tsarin kasa da kasa, za ka kasance cikin jerin abincin da za a ci a teburin." Wannan furucinsa na nuni da irin tunani da alkiblarsu game da hadin gwiwa wadda ke da rauni a tsarin tafiyar da harkokin duniya. Kuma hakan ya sanya kasashe masu tasowa suka rungumi tsarin hadin gwiwar neman ci gaba tare da kasar Sin. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)