logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki a rikicin Ukraine da su kai zuciya nesa

2024-07-10 10:12:01 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya jaddada kira ga sassa masu ruwa da tsaki a rikicin Ukraine, da su yi karatun ta nutsu, su kai zuciya nesa, kana su yi biyayya ga dokokin jin kai na kasa da kasa, tare da kauracewa kaddamar da hare hare kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa.

Yayin da yake tsokaci a jiya Talata a zaman kwamitin sulhun MDD da aka gudanar game da batun Ukraine, Geng ya ce tun bayan tsanantar rikicin Ukraine a watan Fabarairun 2022, tashin hankalin ya haifar da asarar rayukan fararen hula masu yawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Kaza lika tashin hankalin ya sabbaba lalatawa, da rusa dumbin ababen more rayuwa, wanda kuma hakan ya ingiza matsanancin yanayin jin kai wanda mummunan tasirinsa ya fantsama zuwa sassa daban daban.

Geng ya ce game da batun Ukraine, har kullum kasar Sin na fatan a mutunta ikon mulkin kai da tsaron yankunan kasashe daban daban, a kuma nacewa ga ka’idojin yarjeniyoyin MDD, kana a dora muhimmanci ga damuwar tsaro ta dukkanin sassa, tare da goyon bayan matakan shawo kan rikici cikin lumana.  (Saminu Alhassan)