logo

HAUSA

An nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaban kwamitin aiwatar da sabon tsarin kiwon dabbobi a kasar Najeriya

2024-07-10 09:32:58 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zabi tsohon shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaban kwamitin da zai lura da aiwatar da sabuwar manufar tsarin kiwon dabbobi a kasar.

Shugaban ya sanar da nadin tsohon shugaban hukumar zaben ne jiya Talata 9 ga wata, yayin kaddamar da ’yan kwamitin a birnin Abuja. Ya ce. kwamitin shi ke da alhakin samar da mafita na yawan rigingimun makiyaya da manoma a wasu sassan kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda da kansa ne zai jagoranci kwamitin wanda aka zabo wakilai daga ma’aikatu da kamfanoni masu zaman kansu da suke da nasaba da sha’anin noma da kiwo sai kuma gwamnoni na jihohi.

Ya ce, kwamitin har’ila yau shi ne zai kawo karshen matsalolin da suke haifar da cikas wajen samun wadatattun kayan amfanin gona, tare kuma da bullo da wasu damarmaki da zai amfani manoma da makiyaya musamman ta fuskar cinikin nama da madara da kuma kayan abincin dabbobi.

Shugaban wanda ya yi amfani da wannan dama ta kaddamar da ’yan kwamitin wajen sanar da kirkirar wata sabuwar ma’aikatar lura da bukasar sha’anin kiwon dabbobi, inda ya ce, samar da ma’aikata zai baiwa likitocin dabbobi na kasar damar gudanar da binciken su tare kuma da fadada kimiyar jinkirta kwayar halittar nau’ikan dabbobi.

“Akwai bukatar ’yan Najeriya sun yi amfani da wadannan damarmaki ta amfana da sana’ar kiwon dabbobi da samar da madara da sauran albarkatu wanda duka suna da fa’idoji masu yawan gaske a fagen sha’anin kasuwanci da cinikayya. (Garba Abdullahi Bagwai)