logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Guinea Bissau

2024-07-10 20:44:30 CMG Hausa

Da maraicen yau Laraba 10 ga watan nan ne, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Guinea Bissau, Umaro Mokhtar Sissoco Embaló, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar, inda shugabannin biyu suka amince da daga matsayin dangantakarsu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. (Murtala Zhang)