logo

HAUSA

Kasashen Masar da Amurka da Qatar da Isra'ila za su tattauna game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

2024-07-10 11:07:53 CMG Hausa

Tashar talabijin ta Al-Qahera dake kasar Masar, ta ce wakilai daga kasashen Masar, da Amurka, da Qatar da Isra'ila, za su gana a yau Laraba a birnin Doha na kasar Qatar, domin ci gaba da tattaunawa game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Tashar Al-Qahera ta ce wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa, shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Masar Abbas Kamel, da takwaransa na Amurka William Burns ne za su jagoranci tawagogin gwamnatocin kasashen su, bayan kammala wasu zagayen tattaunawa a jiya Talata a birnin Al-Qaheran Masar.

Tattaunawar ta yini biyu a Al-Qahera, ta samu halartar tawagar masu shiga tsakani daga bangaren Isra’ila, karkashin jagorancin shugaban hukumar Shin Bet ta tsaron Isra'ila mista Ronen Bar.

Tun bayan sake barkewar rikicin Gaza a watan Oktoban shekarar 2023, Masar ke shiga tsakani da nufin cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas mai mulki a zirin Gaza, tare da kasashen Amurka da Qatar dake marawa shawarwarin baya.(Saminu Alhassan)