logo

HAUSA

Fakewa da batun kasar Sin ba zai taimaka wa NATO cimma burinta da ya shafi yankin Asiya da tekun Pasifik ba

2024-07-09 21:41:45 CMG Hausa

Za’a kaddamar da taron kolin kungiyar tsaro ta NATO a yau Talata 9 ga wata a birnin Washington dake kasar Amurka. A wajen taron manema labarai da aka shirya kafin taron, babban magatakardan kungiyar, Jens Stoltenberg ya ce, kungiyar na bukatar fadada hadin-gwiwa tare da aminanta dake yankin tekun Indiya da Pasifik, da zummar shawo kan kasar Sin da sauran wasu kasashe, al’amarin da a cewar kafafen yada labarai da dama, yunkuri ne da NATO ta yi ta hanyar fakewa da batun kasar Sin, domin yin shisshigi cikin harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik, da nuna fin karfin Amurka kan sauran kasashe.

A matsayinta na kungiyar da aka kafa bayan yakin cacar baka, kana kungiyar soja mafi girma a duniya, tun kafuwarta har zuwa yanzu, NATO ta zama hanyar da Amurka ke amfani da ita, domin yin fito-na-fito da kawo cikas gami da matsa lamba ga sauran kasashe. A karkashin umarnin Amurka din, sanarwar da aka fitar a wajen tarukan kolin NATO a ‘yan shekarun nan, ta sha rura wutar rikicin dake cewa, wai kasar Sin na haifar da barazana ga duniya, a wani yunkuri na maida kasar abokiyar hamayya, da tilastawa kasashen yankin Asiya da tekun Pasifik su zabi wace za su bi.

Tarihi na tafiya yadda ya kamata. Duk wutar rikicin da NATO ta rura, ba za ta boye gaskiya ba, wato NATO din, kungiya ce da ta wuce yayi, kana, ita ce asalin haifar da barazana ga duk fadin duniya. Manufar NATO kan yankin Asiya da tekun Pasifik, shiri ne dake yunkurin kawo baraka da tada zaune-tsaye har da yake-yake, da nufin taimakawa Amurka nuna babakere a duniya, wadda ta saba wa tarihi, kuma ba za ta yi nasara ba. (Murtala Zhang)