logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kungiyoyin mayaka a jamhuriyar dimokuradiyyar Congo da su gaggauta ajiye makamai

2024-07-09 10:19:27 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce Sin na kira ga daukacin kungiyoyi masu dauke da makamai a jamhuriyar dimokuradiyyar Congo da su gaggauta ajiye makamai, kana su fice  daga yankunan da suka mamaye.

Geng Shuang, wanda ya yi kiran a jiya Litinin, yayin zaman kwamitin tsaron MDD don gane da nazarin halin da ake ciki a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo. Ya jaddada muhimmancin sassan kasa da kasa su goyi bayan dakatar da bude wuta, da kawo karshen dauki ba dadi da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi a kasar.

Jami’in ya ce cikin watanni 3 kacal, dakarun kungiyoyi masu dauke da makamai sun hallaka sama da fararen hula 500, kana tashe-tashen hankula sun tilasawa kimanin mutane miliyan 7.3 rabuwa da muhallansu.

Kaza lika a ranar 3 ga watan nan na Yuli, wasu masu dauke da makamai sun kaiwa wani kamfanin kasar Sin dake jamhuriyar dimokuradiyyar Congon hari, lamarin da ya sabbaba rasuwa da bacewa Sinawa da dama. Kasar Sin ta yi matukar Allah wadai da aukuwar hakan, tana kuma kira da a gaggauta cafke wadanda suka aikata wannan ta’asa, tare da yanke musu hukunci mai tsanani kamar yadda doka ta tanada.

Geng Shuang, ya ce akwai bukatar gaggauta ingiza matakan kwantar da hankula a yankin. A baya bayan nan, ana samun karuwar rashin fahimta da sabani tsakanin kasashen dake shiyyar game da batun gabashin kasar ta jamhuriyar dimokaradiyyar Congo. Don haka kasar Sin ke kara kira ga kasashe masu ruwa da tsaki da su yi hakuri su kai zuciya nesa, kana su warware banbance-banbancen dake akwai ta hanyar tattaunawa, da kaucewa daukar matakan soji. (Saminu Alhassan)