logo

HAUSA

Sin ta kaddamar da mataki na biyu na tallafawa Madagascar shuka shinkafa mai aure

2024-07-09 10:49:09 CMG Hausa

 

Ministar harkokin wajen kasar Madagascar Rasata Rafaravavitafika, da jakadan Sin dake kasar Ji Ping, sun sa hannu kan takardar cimma daidaito kan mataki na biyu na tallafawa Madagascar da aikin shuka shinkafa mai aure, yayin wani biki da aka yi jiya Litinin a ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Tun daga shekarar 2007 zuwa 2011, Sin ta kaddamar da mataki na farko na wannan aiki a Madagascar, inda fadin shinkafar da aka shuka bisa dogaro ga fasahar kasar Sin ya wuce hekta 75,000, kana matsakaicin yawan hatsin da aka girba a kowace hekta ya kai ton 7 zuwa 8, adadin da ya ninka kimanin sau 3 bisa na nau’in wurin.

A wannan mataki na 2 kuma an shirya samar da misalin shuka a yankunan noman shinkafa guda 8 dake fadin tsibirin, kuma kasashen biyu za su gaggauta hadin kai a fannin noman shinkafa mai aure, da laimar kwado, da fitar da amfanin gona zuwa kasar Sin da sauransu, don taimakawa Madagascar wajen tabbatar da samun isasshen hatsi da kuma daga matsayin rayuwar jama’arta.  (Amina Xu)