logo

HAUSA

Shugaban Guinea-Bissau ya jinjinawa gudummawar kasar Sin a fannin bunkasa kasa

2024-07-09 10:27:45 CMG Hausa

Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar kawance ce a fannin hadin gwiwa da kasarsa, kuma ta taka rawar gani wajen bunkasa ci gaban kasar dake yammacin Afirka.

Shugaba Embalo, ya yi tsokacin ne yayin zantawarsa da manema labarai a filin jiragen sama na Bissau, gabanin tasowarsa zuwa nan kasar Sin inda zai gudanar da ziyarar aiki. Ya ce, “Kasashen biyu su kasance kawaye na gargajiya tun farkon gwagwarmayar ’yantar da Guinea-Bissau." (Saminu Alhassan)