logo

HAUSA

Sin ta jaddada fatan warware sabanin cinikayya tsakaninta da EU ta hanyar yin shawarwari

2024-07-09 10:08:14 CMG Hausa

A ranar Lahadin da ta gabata, jakadan kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU Jorge Toledo Albinana ya bayyana cewa, ko da yake cikin watanni da dama da suka gabata, kungiyar EU ta yi ta neman tuntubar kasar Sin kan batun kara yawan haraji kan motoci kirar Sin masu amfani da lantarki ko EVs da ake shigarwa kasashen Turai, sai zuwa kwanan baya ne kasar Sin ta fara neman yin shawarwari kan batun. Dangane da wannan tsokaci, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta bayyana cewa, akwai kuskure a kalaman jakadan.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, tun daga watan Oktoban shekarar 2023, wato lokacin da kungiyar EU ta fara gudanar da bincike kan batun samar da rangwame kan motocin Sin masu amfani da lantarki ko EVs, sau da dama, kasar Sin ta nuna adawarta kan batun, ta kuma sa kaimi ga kungiyar EU da ta daidaita ra’ayinta bisa tushen kare dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Turai, yayin da ake warware sabanin cinikayyar dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari.

Haka kuma, ma’aikatar cinikayyar Sin ta ce, kasar Sin ta riga ta nuna aniyarta, da fatanta na yin hadin gwiwa da kasashen Turai, da kuma gaggauta yin shawarwari kan batun, domin cimma matsayi daya mai dacewa da moriyar bangarorin biyu. A sa’i daya kuma, kasar Sin za ta dauki matakai gwargwadon bukata, da mai da martani ga wadanda suka bata ka’idoji, da kuma matsa wa kasar Sin lamba ta hanyar da ba ta kamata ba.  (Mai Fassarawa: Maryam Yang)