logo

HAUSA

Ecowas ta nemi shugabannin Senegal da Togo da su kula da aikin dakatar da ficewar kasashen Mali da Niger da Burkina Faso daga kungiyar

2024-07-09 10:17:08 CMG Hausa

Shugaban kungiyar Ecowas karo na biyu, kana shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zabi shugabannin kasashen Senegal da Togo Bassirou Faye da Faure Gnassingbe a matsayin manzannin musamman da za su dakatar da kasashen Mali da Niger da kuma Burkina-Faso daga ficewa daga cikin kungiyar.

A yayin jawabinsa na farko bayan sake zabarsa da aka yi a birnin Abuja a matsayin shugaban kungiyar ranar Lahadi 7 ga wata, shugaba Bola Ahmed ya ce, babu yadda za a yi kungiyar ta amince a ci gaba da samun baraka a tsakanin mambobi kasashen.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Shugaba Bola Ahmed Tunibu ya bukaci shugabannin kasashen biyu da su yi aiki tukuru a matsayinsu na manzannin musamman na kungiyar ta Ecowas wajen hakurkuntar da shugabannin kasashen Mali da Jamhuriyyar Nijar da kuma Burkina Faso domin dai su sauya shawarar da suka dauka na yanke alaka da kungiyar ta Ecowas.

Ya ce, dukkannin shugabannin kasashen uku ’yan uwanmu kuma ba za a bar su su zartar da shawarar da ko kadan ba za ta yi wa al’umomin kasashensu dama na sauran kasashen dake shiyyar dadi ba.

Ya kuma baiwa manzannin musamman din damar tuntubar sa ko kuma hukumar gudanarwar kungiyar ta Ecowas a duk abin da ya gagare su a aikin da aka ba su.(Garba Abdullahi Bagwai)