logo

HAUSA

Har Kullum Babbar Kasa, ita ce mai kulawa da kanana

2024-07-09 19:41:46 CMG Hausa

Yayin wani zaman Kwamitin Sulhu na MDD don gane da nazarin halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya jaddada kasa da kasa su goyi bayan dakatar da bude wuta, da kawo karshen dauki ba dadi da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi a kasar.

Yanayin da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ke ciki, batu ne mai tayar da hankali ganin yadda kasar ta shafe sama da shekaru 30 tana fama da rikici, inda kuma a baya-bayan nan yanayin ya kara tsanani. Ba sai an fada ba, kowa ya san illar da rikici ke haifarwa, kama daga rashin matsuguni da na abinci, zuwa rashin ci gaba da sauransu, bare irin wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.

A cewar Geng Shuang, cikin watanni 3 kacal, dakarun kungiyoyi masu dauke da makamai sun hallaka sama da fararen hula 500, kana tashe-tashen hankula sun tilasawa kimanin mutane miliyan 7.3 rabuwa da muhallansu. Wannan kadai ya isa tunatar da al’ummar duniya cewa, wannan kasa da jama’arta na matukar bukatar dauki.

Sai dai a halin yanzu, wasu manyan kasashen duniya sun fi mayar da hankalinsu ga yada jita-jita da babakere, sun manta da nauyin da ya rataya a wuyansu na taimakawa juna, musammam kasashe masu karamin karfi. Maimakon taimakawa irin wadannan kasashe, sai ake mayar da hankali wajen abubuwa marasa muhimmanci.

Duk wanda ke bin yanayin harkokin duniya, zai yarda da cewa, kasar Sin ce kullum kan tuna da yanayin da kasashen Afrika ke ciki, kuma ita ce kullum ke tsaya musu da neman hanyoyin da za su warware matsalolinsu da kansu, ba tare da ta gindaya musu wasu sharudda na siyasa ko tsoma bakin cikin harkokinsu na gida ba. Wannan dalili ne ya sa a kullum nake kiran kasar Sin da babbar kasa da ta san ciwon kanta, kuma mai kulawa da na kasa da ita, duk da cewa ita ma tana da aiki a gabanta na raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummarta, ba ta taba mantawa da taimakawa kasashe mabukata. Duk yadda mutum ya kai ga son zuciya ko yin karya, ba zai taba iya karyata manufar taimakon Sin ga kasashen Afrika, wato niyyarta na ganin sun samu ci gaba da zaman lafiya.

Fatan ita ce, kasashen duniya za su amsa kira, su kuma mayar da hankali kan abubuwa mafiya muhimmanci da duniya ke bukata, don ganin jama’a sun rayu cikin kwanciyar hankali da wadata, domin hannu daya, ba ya daukar jinka-wato kasar Sin kadai, ba za ta iya daukar nauyin daidaita matsalolin duniya baki daya ba.