logo

HAUSA

Sojojin Amurka sun janye daga sansanin sojin sama a Nijar

2024-07-09 10:18:23 CMG Hausa

A ranar 7 ga wata ne ma’aikatar tsaron Nijar da ma’aikatar tsaron Amurka suka sanar da cewa sojojin Amurka sun janye jiki daga sansanin sojin saman Nijar mai lamba 101 dake Yamai. Kuma za su fice gaba daya daga kasar ta Nijar kafin ranar 15 ga watan Satumba na wannan shekara.

Sanarwa da kasashen biyu suka fitar tare ta ce, sojojin Amurka sun kammala janye jiki tare da kayan aikinsu daga sansanin sojin sama mai lamba 101 dake Yamai, kuma mataki na gaba shi ne janyewa daga sansanin sojin sama mai lamba 201 dake Agadez.

Daga bisani a wannan rana, rukunin karshe na sojojin Amurka dake sansanin sojin saman Yamai mai lamba 101 sun tashi a jirgin sama. Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasar sun ce sojojin Amurka kusan 950 ne ke jibge a Nijar, kuma kusan mutane 760 aka janye tun bayan da sojojin Nijar suka bukaci janyewar sojojin Amurka. A wani labarin kuma, jami’an da ke kula da gudanar da ayyukan janyewar a Amurka a ranar 5 ga wata, sun ce za a iya kammala janyewa daga sansanin na 201 a watan Agusta. (Mohammed Yahaya)