logo

HAUSA

Sin ta gabatar da sabuwar fasahar bincike da bayyana harkokin sararin samaniya

2024-07-09 11:25:50 CMG Hausa

Yayin babban taron bayani game da harkokin sararin samaniya na shekarar 2024, wato taron kolin harkokin sadarwa na duniyarmu da ya gudana a jiya Litinin, masanan kimiyya da fasaha na kasar Sin, sun gabatar da sabuwar fasahar bincike da bayyana harkokin sararin samaniya da za a yi amfani a harkokin kasuwanci.

An fidda sabuwar fasahar ne mai lakabin “GEOVIS”, bisa fasahar tattara da daidaita bayanan taurarin dan Adam. Cikin sabuwar fasahar da aka fidda, an kara wasu ayyukan da suka hada da bincike da yin nazari kan harkokin sadarwar taurarin dan Adam, da kuma tsara falakin binciken sararin samaniya mai zurfi da dai sauransu. Haka kuma, an kyautata aikin yin gargadi kan hadarin yin karo, domin biyan bukatun daidaita zirga-zirgar taurarin dan Adam masu dimbin yawa cikin sararin samaniya.

Ban da haka kuma, wata sabuwar na’ura ta zamani da aka kera bisa fasahar tattara da daidaita bayanan taurarin dan Adam, tana iya gudanar da ayyukan bayyana yanayin sararin samaniya dake kusa da doron duniyarmu, da tsara hanyoyin jiragen sama da kanta, da kuma ba da taimako kan harkokin zirga-zirgar jiragen cikin sararin samaniya dake kusa da doron kasa da dai sauransu, domin ba da goyon baya mai karfi ga aiwatar da harkokin sararin samaniya a kusa da doron kasa, yayin da kuma ake samar da hidimomi ga masu bukata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)