logo

HAUSA

An sake zabar shugaban Najeriya a matsayin shugaban ECOWAS, ya kuma nanata kira kan samar da rundunar ko-ta-kwana

2024-07-08 09:48:16 CMG Hausa

Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu a jiya Lahadi ya yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da su hada kai wajen kafa rundunar ko-ta-kwana da kuma dorewarta a yankin domin tinkarar barazanar matsalar tsaro da ke kara kamari a yankin.

A cikin jawabinsa na bude taron majalisar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS karo na 65 a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Tinubu wanda aka sake zabarsa a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS a ranar Lahadi, ya bayyana muhimmancin kafa rundunar ko-ta-kwana, ya kuma bukaci kasashe mambobin kungiyar da su kara himma wajen samar da albarkatun da ake bukata domin tabbatar da tsaron yankin. (Yahaya)