logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya aike da sakon taya murna ga taron kare muhalli na kungiyar hadin kai ta Shanghai

2024-07-08 11:42:24 CMG Hausa

A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron kare muhalli na kungiyar hadin kai ta Shanghai.

Cikin wasikar, shugaba Xi ya bayyana cewa, kare muhalli da inganta ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, matsaya ce da kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai suka cimma. Ya ce a shekarun baya-bayan nan, Sin ta nacewa bin tafarkin neman ci gaba irin na zamani, wanda ya hada da sabunta dabarun samar da kayayyaki da rayuwa cikin wadata da kyakkyawan muhalli, kuma ta samu nasarorin da suka ja hankalin duniya baki daya. A cewarsa, a karkashin wannan dandali, kasar Sin na fatan karfafa musaya da hadin gwiwa da dukkan bangarori a fanin kare muhalli, domin samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai dorewa a kasashe daban-daban da kuma jituwa tsakanin dan adam da sauran halittu.

A yau Litinin ne aka bude taron a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin. Taken taron shi ne “Hada hannu domin raya muhalli da inganta jituwa tsakanin dan adam da sauran halittu”.  (Fa’iza Mustapha)