An nada shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin manzon musamman na CEDEAO game da kungiyar AES
2024-07-08 19:28:44 CMG Hausa
A yayin zaman taron kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika CEDEAO ko ECOWAS da aka bude a ranar jiya Lahadi 7 ga watan Yuli, shugabanni da gwamnatocin kasashen wannan kungiyar sun tabo makomar dangantakarsu da kungiyar AES a nan gaba.
Daga birnin Yamai abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan aiki.
A yayin wannan zaman taro karo na 65 na shugabannin kasashe da gwamnatocin gamayyar tattalin arziki na kasashen yammacin Afrika CEDEAO ko ECOWAS da ya gudana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, a karashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, shugaban karba karba na kungiyar ECOWAS. Da yake jawabi, shugaban kwamitin kungiyar, Alieu Tourey ya maida hankali kan illolin ficewar kasashen uku Nijar, Burkina Faso da Mali, musammun kan batun shige da fice na mutane da dukiyoyinsu a cikin shiyyar yammacin Afrika da ke fama da matsalar tsaro, sauyin yanayi da tattalin arziki mai rauni sosai. Haka kuma ya kara tunatar da muhimmancin manyan ayyukan zuba jari na bankuna biyu na shiyyar BIDC da BOAD a cikin wadannan kasashe uku.
A yayin kammala taron karo na 65, shugaba Bola Tinubu ya nada shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, a matsayin manzon musamman game da kasashen AES inda sojojin da suka yi juyin mulki domin ganin yadda dangantaka za ta kasancewa da wadannan kasashe uku.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.