logo

HAUSA

Za a kammala aikin ginin hedikwatar kungiyar Ecowas da ake ginawa bisa tallafin kasar China cikin shekara ta 2025

2024-07-08 09:51:11 CMG Hausa

Ministan harkokin kasashen waje na tarayyar Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana sabon ginin hedikwatar kungiyar Ecowas a matsayin idon yammacin Afrika wanda yake kunshe da dabi’u da al’adun gargajiya na daukacin al’umomin yankin.

Ya bayyana hakan ne a karshen mako lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron karamin kwamitin ministoci a game da aikin ginin hedikwatar kungiyar ta Ecowas a birnin Abuja. Ya ce, an aza tubalin fara ginin ne a watan Nuwanban 2022 kuma an tsara kammalawa a watan Fabarailun 2025.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar wanda kuma shi ne shugaban majalissar ministocin kungiyar, ya ce, hakika tsarin ginin yana nuni da kyakkyawar makoma ga Afrika, kuma ofishin zai kasance wani tushe babba na samar da hadin kai da bunkasar tattalin arziki da tsaro a nahiyar baki daya.

Ministan harkokin kasashen wajen na Najeriya ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa takwarorinsa bisa ci gaba da ingiza tsare-tsaren da za su tabbatar da kasancewar yankin a dunkule.

A yayin taron ministocin kungiyar ta Ecowas, mataimakiyar shugaban hukumar kungiyar Madam Damtien Tchintchibidja yabawa gwamnatin Najeiya ta yi bisa samar da filin da ake aikin ginin hedikwatar hukumar tare kuma da cire duk wani haraji na shigo da kayayyakin aikin ginin.

Ha’ila yau ta mika godiya ta musamman ga gwamnatin kasar China saboda gudummawarta wajen aikin ginin hedikwatar bisa tallafin kasashen dake cikin kungiyar.

Ana dai gudanar da aikin ginin ne da kudaden da gwamnatin kasar China ta bayar ta hannun hukumar bunkasa kasashe da hadin kai na kasar Sin. (Garba Abdullahi Bagwai)