logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga sabon gwamnan tsibiran Solomon

2024-07-08 11:15:02 CMG Hausa

 

Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa David Tiva Kapu sakon taya murnar kama aiki a matsayin gwamnan kasar tsibiran Solomon.

Xi Jinping ya bayyana a cikin sakonsa cewa, Sin na daukar batun bunkasa huldar kasashen biyu da muhimmanci, yana kuma fatan kara hadin kai da gwamnan don gaggauta daukaka huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannnoni dake tsakaninsu a sabon zamani, zuwa wani sabon matsayi, ta yadda za ta amfanawa al’umomminsu. (Amina Xu)