Dalibai ’yan Najeriya 74 da suka samu kwarewar tukin jirgin kasa a China sun dawo gida
2024-07-08 09:53:29 CMG Hausa
Gwamnatin Najeriya ta karbi dalibai 74 ’yan Najeriya da suka samu kwaraewa kan tukin jirgin kasa da kuma gyaransa a kasar China karkashin kulawar kamfanin gine gine na CCECC.
Yayin wata liyafar maraba da aka shirya musu a birnin Abuja a karshen makon jiya, ministan sufuri na kasar Sanata Sa’idu Alkali ya kara jaddada kudurin gwamnati na kwadaitawa ’yan Najeriya sha’awar shiga harkokin sufurin jiragen kasa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan wanda ya bayyana tasirin sufurin jiragen kasa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa, wanda wannan ce ta sanya ma gwamnati sanya batun cikin shirin samar da ababen more rayuwa na kasa ta hanyar kulla yarjejeniya da kasar China bisa manufar amfani da kayan gida a dukkannin harkokin raya kasa.
Sanata Sa’idu Alkali ya ce, tuni gwamnati ta fara ganin fa’idar wannan yarjejeniya musamman ma amincewar kamfanin gine-gine na CCECC mallakin ’yan kasuwar kasar China ya yi wajen daukar dawainiyar matasa ’yan Najeriya domin dai ba su horo a kan sha’anin sufurin jiragen kasa, wanda wannan na daga cikin ayyukan taimakon raya kasa da kamfanin ke yi a Najeriya.
A jawabinsa shugaba kamfanin gine-ginen na CCECC reshen Najeriya Mr Jason Zhang kara jaddada kudirn kamfanin ya yi na kara kyautata alaka tsakanin Najeriya da kasar China, inda ya ce, wannnan bikin na tarbar daliban da suka sami horo a kasar China, wata babbar alama ce dake kara tabbatar da cewa akwai mu’amulla ta kut-da kut tsakanin kasashen biyu tun da dadewa. (Garba Abdullahi Bagwai)