logo

HAUSA

Wang Lijun dake kokarin taimakawa manoma wajen sayar da hatsi

2024-07-08 15:34:13 CMG Hausa

Kasar Sin dai na daukar al'umma a matsayin ginshikinta, sannan jama'a na daukar abinci a matsayin rayuwarsu. Ta yaya za a aiwatar da dokar ba da tabbaci wajen samun isasshen abinci, da tabbatar da gudanar da harkokin kasuwancin hatsi, da inganta samun karuwar hatsi, da kuma taimakawa manoma wajen kara samun kudin shiga? Wang Lijun, ‘yar kasar Sin da ta fito daga lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar ta ba da amsa kan haka. 

Gundumar Tailai da ke birnin Qiqihar na lardin Heilongjiang, babbar gunduma ce ta fuskar aikin gona, gundumar tana samar da shinkafa mai inganci kusan ton miliyan 1.8 da kuma masara kimanin ton dubu 800 a duk shekara, don haka, ana kiranta da "Garin Kifi da Shinkafa" a arewacin kasar Sin. Haka kuma shinkafar Tailai ta sami kariya ta Samfurin Alamar Yanki ta Kasa, da Tambarin Alamar Yanki.

A baya, manoma a gundumar Tailai sun taba fuskantar matsalar sayar da hatsi sakamakon wasu abubuwa daban daban, ciki har da rashin samun bayanai. A duk lokacin kaka, a kan samu wasu ''dillalai'' masu sayo hatsi da suke zuwa kauyukan dake gundumar, suna sayan hatsi daga hannun manoma a kan farashi mai rahusa, sannan su sayar wa masu sana’ar hatsi a farashi mai tsada, don samun riba sakamakon irin gibin dake kasancewa kan farashin hatsi. Hakan ya sa manoma ba za su iya sayar da hatsin su a kan farashi mai kyau ba, baya ga haka ya yi mummunan tasiri ga daidaiton farashin kasuwar hatsi na wurin.

A shekarar 1998, Wang Lijun ta kafa Kamfanin Amfanin Noma na Diwang na gundumar Tailai, wanda ya tsunduma cikin sayan danyen hatsi kamar masara da shinkafa. A cikin shekaru 20 da wani abu da suka wuce, kamfaninta ya taimakawa manoma da yawa wajen warware matsalolin da suke fuskanta a fannin sayar da hatsi.

Wang Lijun ta ce, “Manoman su kan kwashe shekara guda suna aiki tukuru, kuma suna fatan sayar da hatsin su a farashi mai kyau. A Lokacin da muke sayen hatsi daga hannayen su, muna mai da hankali ga tsare gaskiya, da amana, da bayar da farashin da ya dace, don haka, manoman wurin sun amince da mu sosai.”

Wang Lijun ta bayyana cewa, domin kara karfafa gwiwar manoma, sun bullo da wasu sabbin nau'o'in iri, da sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da manoma, da kuma wani nau'i na "kwangilar noma", inda a matakin farko na dashe, za su tabbatar da wane irin nau’in hatsi ne suke bukata, sannan sai a noma irin wadannan hatsi, ta hakan manoma ba za su damu da matsalar sayar da hatsin su ba. Wannan tsarin ba wai kawai ya baiwa manoma damar kwantar da hankali wajen yin shuka ba, har ma yana karfafa musu gwiwar ci gaba da fadada aikin noma da kara samar da hatsi mai yawa.

Lokacin da aka sami hawa da saukar farashin hatsi, Wang Lijun ta kan dage kan gudanar da kasuwanci bisa gaskiya da amana. A yayin da ake samun hauhawar farashi, Wang Lijun ta kan daidaita farashin sayen hatsi daga hannun manoma bisa halin da ake ciki, a yayin da ake samun saukar farashi kuma, za ta biya ne bisa ga farashin da suka amince da su tun farko don tabbatar da samun kudin shiga ga manoma.

A wata shekara, farashin shinkafa a kasuwa ya fadi sosai, lamarin da ya sa manoman suka fuskanci matsaloli wajen sayar da hatsi, kuma sun damu cewa, ba za su samu riba ba bayan shafe shekara guda suna aiki. Sun kuma nemi taimakon Wang Lijun. Bayan fahimtar farashin da manoma ke iya karba, sai Wang Lijun ta tuntubi dillalai da sassan gwamnati don daidaita farashi da hanyoyin tallace-tallace. Ta hanyar iyakacin kokarin da ta yi, an kai ga shawo kan matsalolin da manoma suka fuskanta a lokacin.

Wang Lijun ta kara da cewa, akwai misalai kamar haka da yawa. Sa’ad da manoma suka gamu da wahala wajen sayar da hatsi, za mu ba da taimako kuma mu yi iyakacin kokarinmu don taimaka musu wajen magance matsalolinsu. A cewar ta, ayyukan da muke yi ba wai kawai suna da alaka da rayuwar manoma da noman hatsi da samarwa da sayar da hatsi ba, har ma da samar da tabbaci a kasuwar hatsi.

A yanzu haka, kamfanin Wang Lijun ya kafa wani tsarin hadin kai na "kasuwanci da kungiyoyin hadin gwiwa da manoma" tare da wasu kungiyoyin hadin gwiwa na fasaha, da kuma sanya hannu kan kwangilolin sayayya, kana da ba da hidimar musamman a fannonin adanawa da busar da hatsi da dai sauransu, don samar da sauki ga manoma wajen sayar da hatsi.

Baya ga haka kuma, kamfaninta ya kafa sansanonin shuka guda 25 a gundumar Tailai, tare da tallafawa manoma wajen kafa gonaki fiye da eka dubu 20, da kuma jagorantar manoma sama da 3,500 wajen kara samar da hatsi da kara samun kudin shiga. A lokacin da ake shan aikin sayen hatsi, manyan motocin jigilar hatsi su kan yi dogon layi a gaban kofar kamfanin ta.

Wang Lijun ta ce, “A da, mu kan sayar da hatsi ta hanyar wasu masu rarrabawa da masu shiga tsakani, wadanda suke samun riba sakamakon bambance-bambancen farashin hatsi. Amma, yanzu muna yin hadin kai da kungiyoyin hadin gwiwa, don sayar da hatsin manoma ga kamfanoni kai tsaye, ta hakan manoman suna kara samun kudin shiga da kuma wadata.”

Wang Lijun tana daya daga cikin mata “masu sayar da hatsi” a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Heilongjiang wani babban lardi ne na noma, wanda adadin hatsin da ya samar a shekarar 2023 ya kai kilogiram biliyan 155.76, wanda ke matsayi na farko a kasar a cikin shekaru 14 da suka wuce a jere. A wannan yanki, “masu sayar da hatsi” suna kokarin tabbatar da raya masana’anta mai inganci, da kuma inganta samar da guraban ayyukan yi.