logo

HAUSA

Rundunar sojin kasar Sin da take tabbatar da zaman lafiya a kasar Lebanon ta samu lambar yabo ta kare muhalli daga UNIFIL

2024-07-08 08:20:52 CMG Hausa

A ran 27 ga watan Yunin da ya gabata, rundunar sojin kasar Sin karo na 22 da take tabbatar da zaman lafiya a kasar Lebanon a madadin MDD ta samu lambar yabo ta matsayin farko ta kare muhalli daga UNIFIL domin nuna mata yabo da ta taka muhimmiyar rawa wajen kare muhallin inda rundunar take. An labarta cewa, UNIFIL tana kunshe da sojojin daga kasashe 49, kowace shekara tana ba da wannan “lambar yabo ta kare muhalli” sau daya. (Sanusi Chen)