logo

HAUSA

An kammala babban taron farko na shugabannin kasashen kungiyar AES

2024-07-07 16:43:10 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, an kammala babban taron farko na shugabannin kasashen kungiyar AES, a birnin Yamai a ranar jiya Asabar 6 ga wata, tare da fitar da sanarwar karshe mai sunan sanarwar birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shugabannin rikon kwarya na kasashen kungiyar yankin Sahel AES, kanal Assimi Goita na Mali, kaftin Ibrahim Traore na Burkina Faso da janar Abdrouhamane Tiani na Nijar, suka yi babban taron farko na kungiyar AES a Yamai, babban birnin kasar Nijar a ranar jiya 6 ga watan Yuli. Ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare ya karanta sanarwar karshe. A cikin wannan sanarwa, ministan harkokin wajen Nijar ya sake ambato babban burin da kungiyar kasashen yankin Sahel na kafa wata gamayyar tattalin arziki da kudi bisa turba mai kyau.

A cikin manyan batutuwa 25 da suka kunshi wannan sanarwar karshe, akwai batun kafa wata gamayyar tattalin arzik domin ci gaban kasashen AES, kafa wani bankin AES, haka kuma sanarwar ta yi tsokaci kan matsalar tsaro da kasashen yankin Liptako suke fuskanta duk da kokarin da suke yi na kawo karshen ta’addanci ta yadda al’ummomin kasashen uku za su yi rayuwa cikin jin dadi da walwala, haka kuma sanarwar karshen ta umurni ministocin kudi da su fito da wani jadawali cikin gaggawa wanda zai aza alkibla mai kyau game da amfani da albarkatun muhalli da arzikin ma’adinai, da sauran arzikin karkashin kasa da Allah ya hore ma kasashen Afrika, musamman ma na yankin Sahel.

Daga karshe, shugabannin kungiyar ta kasashen yankin Sahel sun zabi shugaban kasar Mali, Assimi Goita a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar AES tare da daukar alkawarin sake yin wata haduwa a shekarar 2025.