An kaddamar da taron kungiyoyin siyasa da na fararen-hula na Sudan a kasar Masar
2024-07-07 16:18:16 CMG Hausa
An kaddamar da taron kungiyoyin siyasa da na fararen-hula na kasar Sudan a Alkahira, babban birnin kasar Masar, a jiya Asabar 6 ga wata. Taron na yini biyu, wanda gwamnatin Masar ta karbi bakuncinsa, ya samu halartar wakilai da dama daga wasu kungiyoyin siyasa da na fararen-hula na Sudan, da wakilan kungiyoyin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afirka da sauransu.
Makasudin shirya taron shi ne, hada kawunan kungiyoyin fararen-hula da na siyasa na kasar Sudan, don lalubo bakin zaren warware rikicin kasar, da sassauta matsalar jin-kai dake addabar kasar. A wajen bikin bude taron, ministan harkokin wajen Masar, Badr Abdelatty, ya yi kira ga bangarori masu gaba da juna a Sudan, da su tsagaita bude wa juna wuta, inda ya jaddada cewa, ya zama dole a nemo mafita ga rikicin Sudan, karkashin ka’idojin girmama cikakken mulkin kai, da yankin kasa, da kauce wa yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar. Kaza lika, Masar za ta ci gaba da yin kokari tare da sauran wasu bangarori, don kawo karshen rikicin Sudan ba tare da bata lokaci ba, da kare muradun al’ummar kasar. (Murtala Zhang)