logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Iran

2024-07-06 19:37:04 CMG Hausa

Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Masoud Pezeshkian domin taya shi murnar lashe zabe a matsayin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A wannan rana, Xi Jinping ya koma birnin Beijing cikin jirgin sama na musamman bayan halartar taron majalisar shugabannin kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO karo na 24, da ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Tajikistan. (Safiyah Ma)