logo

HAUSA

Hadin gwiwa tsakanin Sin da Tajikistan zai haifar da sabuwar makoma

2024-07-06 20:16:26 CMG Hausa

A ziyarar da shugaban kasar Sin Xi jinping ya kai kasar Tajikistan daga ranar 4 zuwa ta 6, kasashen biyu sun ba da sanarwar kafa cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a wannan sabon zamani.

Ba shakka dangantakar dake tsakanin Sin da Tajikistan zai iya kaiwa wani sabon matsayi saboda harkokin diflomasiyyar shugabannin kasashen biyu suna taka muhimmiyar rawa. Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashen biyu sun gana da juna fiye da sau 10. Inda suka kulla abota mai zurfi, da sa kaimi ga ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Tajikistan.

A yau, kasar Sin ta himmatu sosai wajen inganta aikin zamanantar da kasar, kana Tajikistan ma tana kokarin cimma “Dabarun raya kasa kafin shekarar 2030”. Wannan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ya dace da bukatun ci gaban kasashen biyu, kuma ya yi daidai da muradunsu na bai daya. (Yahaya)