logo

HAUSA

Shugaban Burkinafaso ya isa Yamai domin halartar taron koli da shugabannin Nijar da Mali

2024-07-06 15:42:30 CMG Hausa

Shugaban rikon kwarya na Burkinafaso Ibrahim Traore, ya isa birnin Yamai da yammacin jiya Juma’a domin halartar taron koli tare da shugabannin kasashen Nijar da Mali.

Traore wanda takwaransa na Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani ya tarba a filin jiragen sama na kasa da kasa na Diori Hamani, zai halarci taron koli na farko na kungiyar hadin kan kasashen Sahel a safiyar yau Asabar, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Taron wanda kuma zai samu halartar Assimi Goita, shugaban rikon kwarya na kasar Mali, zai tattauna batutuwa da kalubalen da kasashen uku ke fuskanta wadanda suka hada da tsaro da kariya, da yaki da ta'addanci, da mu’amalar tattalin arziki, al’adu da kasuwanci.

Burkina Faso, Mali da Nijar sun kafa kawancen kasashen Sahel wato yarjejeniyar kare juna, a watan Satumban 2023, tare da sanar da ficewarsu daga kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka a farkon wannan shekara. (Yahaya)