logo

HAUSA

Shugabar Peru: Ajandar duniya da shugaba Xi ya gabatar na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar duniya

2024-07-06 15:15:09 CMG Hausa

A 'yan kwanakin da suka gabata, shugabar kasar Peru Dina Boluarte ta yi hira da wani dan jarida daga babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, inda ta ce, ajandar duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar duniya.

Boluarte ta bayyana cewa, wannan ita ce ziyararta ta farko a kasar Sin bayan da ta hau kan karagar mulki a matsayin shugabar kasar Peru, kuma saurin bunkasuwar kasar Sin yana da ban mamaki. Ta ce, a cikin shekaru 40 da suka wuce, kasar Sin ta gina birnin Shenzhen daga tushe, kuma saurin bunkasuwarsa a bangaren fasahohin zamani na da ban mamaki kwarai da gaske.

Ta kara da cewa, tana fatan kasar Peru za ta iya hadewa a matsayin wata kasa, da rage gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta, da kuma ci gaba da zama kasa mai ci gaban masana'antu kamar kasar Sin mai fasahahohin dijital da AI da kuma masana’antu.

Yayin da ta ambaci shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta ce, wannan shugaba mai kishin ci gaban kasa yana kaunar jama'arsa, kuma ya kamata a yi koyi da shi. Karfin shugabancin shugaba Xi Jinping da ajandar duniya da ya gabatar suna da matukar ma'ana ga zaman lafiya a duniya, kuma ta yaba da wadannan tsare-tsare.(Safiyah Ma)