logo

HAUSA

Kasar Sin ta ware kudade don aikin agajin bala’u

2024-07-06 15:57:57 CMG Hausa

Ma’aikatar kudi ta kasar Sin da ma’aikatar ba da agajin gaggawa ta kasar a yau Asabar sun ware kudi Yuan miliyan 540, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 75.75 don tallafawa kananan hukumomi domin gudanar da ayyukan agajin bala’u da suka shafi ambaliyar ruwa, bala’o’in da suka shafi kasa da muhalli da gobarar daji.

Yuan miliyan 503 musamman, za a ba su ga tallafin bala'in ambaliyar ruwa da bala'o'i da suka shafi kasa da muhalli domin gudanar da bincike, ceto da sake tsugunar da mazauna larduna tara da suka hada da Hunan, Anhui, da Jiangxi, yayin da za a ware yuan miliyan 37 don mayar da martani ga gobarar daji a Mongoliya ta gida da Shanxi, a cewar ma'aikatar kudi.

Cibiyar kula da yanayi ta kasar Sin a yau Asabar din ta fitar da sanarwar cewa, za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar. (Yahaya)