logo

HAUSA

Shugaba Tinubu ya kaddamar da majalissar bunkasa tattalin arzikin kasa

2024-07-06 14:38:38 CMG Hausa

A ranar alhamis 4 ga wata shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci bikin kaddamar da ’yan majalissar lura da cigaban tattalin arzikin kasar.

Majalissar mai wakilai 31 an kaddamar da ita ne a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, inda mambobin majalissar suka kunshi mataimakin shugaban kasa, da shugaban majalisar dattawa da shugaban kungiyar gwamnonin kasar da sauran manyan masu masana`antu da shugabannin wasu bankuna, kuma shugaban kasa Bola Tinubu ne zai kasance shugaban majalissar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A jawabin sa yayin kaddamar da `yan majalissar shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana daga cikin babban aikin `yan majalissar lalubo hanyoyin fita daga munmunan yanayin da tattalin arzikin kasar ya shiga. 

Yayin kaddamar da `yan kwamatin, shugaban na tarayyar Najeriya ya gabatar da sakamkon nazarin da gwamnati ta yi a wasu fannonin tattalin arziki da nufin kawo cigaba wanda ake sa ran za a samar da naira tiriliyan biyu cikin wasu bangarori na tattalin arzikin nan da watanni shida masu zuwa, wannan kamar yadda shugaban ya fada zai rage tsadar rayuwar da `yan Najeriya ke fuskanta sakamakon sauye sauyen tattalin arziki da gwamanti ta bijiro da su.

“ Na yi imanin sosai wajen samun hadin gwiwa da kamfanonin masu zaman kansu wajen gudanar da sauye-sauye a tattalin arziki , a inda gwamnati za ta bayar da tallafi a wuraren da suka zama wajibi sannan kuma a bar kasuwa ta sarrafa tsarin farashin da ya kamata” 

Ministan kudi Mr Wale Edun ya yi karin haske a game da adadin da kowanne fanni zai amfana daga naira tiriliyon biyun da za`a kashe nan da watanni 6.

“Naira tiriliyon biyu da za a kebe domin tallafawa bangarorin tattalin arziki, ya kunshi naira buliyan 350 ga bangaren kiwon lafiya da kyautata walwalar al`umma, sai buliyan 500 harkokin noma da samar da abinci ,sai wata buliyan 500 ga bangaren makamashi da sha`anin wutan lantarki, yayin da kuma za a kashe naira buliyan 650 wajen tallafawa sauran fanonin kasuwanci”(Garba Abdullahi Bagwai)