logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya ba da umarni kan aikin tinkarar ambaliyar ruwa a kasar Sin

2024-07-06 14:57:22 CMG Hausa

A jiya Juma'a bisa agogon kasar Sin, ambaliyar ruwa ta tsaga kan gabar ruwa a wani bangaren tabkin Dongting dake garin Yueyang na kasar, daga baya ruwan da ya fito daga tsagar ya mamaye wasu gonaki. Zuwa yanzu, an riga an kaurar da dukkan mutanen wurin da ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Abkuwar lamarin ya janyo hankalin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a ketare a lokacin. Daga baya shugaban ya ba da umarnin cewa, ya kamata a kaurar da dukkan jama'ar da bala'in ya ritsa da su, gami da tsugunar da su yadda ya kamata. Kana, kamata ya yi, a yi iyakacin kokarin tinkarar ambaliyar ruwan don kare rayukan jama'a da kuma dukiyoyinsu, inda babbar hukumar kasar mai kula da aikin tinkarar bala'in ambaliyar ruwa za ta tura tawaga zuwa wurin da bala'in ya abku don jagorancin aikin kai dauki ga jama'a. Ban da haka, shugaban ya bukaci gwamnatocin kasar da su tura karin mutane don karfafa aikin sintiri da sanya ido kan gabar koguna, don tabbatar da cewa za a tinkari bala'in ambaliyar ruwa ba tare da bata lokaci ba.

Ban da haka, a nata bangare, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin tana sanya ido kan nau'ikan abinci da kayayyakin masarufin da ake bukata a wuraren kasar da suka fi fama da ambaliyar ruwa a kwanakin nan, inda take jagorancin aikin jigila da ajiyar dimbin abinci da kayayyakin da ake bukata, don riga kafin matsalar samar da kayayyakin da ka iya bullowa. (Bello Wang)