logo

HAUSA

Kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ya amince da rahoton kasar Sin na kare hakkin dan Adam

2024-07-05 11:11:10 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ya kammala aikin nazarin gama-gari na lokaci-lokaci na UPR karo na hudu ga rahoton kasar Sin na kare hakkin dan Adam, wanda ya kammala lami lafiya kuma cikin nasara, a cewar shugaban tawagar kasar Sin.

A yayin taron UPR din nan, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland Chen Xu ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin kan shawarwarin da kasashe daban daban suka bayar a lokacin zaman UPR, da kuma ci gaban da aka samu kan sabbin matakan hakkokin bil Adama guda 30 da kasar Sin ta kuduri aniyar aiwatarwa.

A gun taron, kasashe da dama irin su Rasha, Venezuela, Uzbekistan, Gambiya, da Vietnam, sun darajanta kokari da nasarar da kasar Sin ta samu wajen ciyar da hakkin dan Adam gaba.

Bayan da aka amince da rahoton na kasar Sin, taron ya tashi tsaye da tafi da murna, kuma wakilan kasashen da dama sun mika sakon taya murna ga tawagar kasar Sin. (Yahaya)