Xi ya halarci bikin maraba da shugaban Tajikistan ya shirya masa
2024-07-05 19:13:52 CMG Hausa
A Juma’ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin maraba da shugaban kasar Tajikistan Emomali Rahmon ya shirya masa a birnin Dushanbe fadar mulkin kasar, bayan da shugabannin biyu suka yi kwarya-kwaryar tattaunawa.
Kaza lika, a dai birnin na Dushanbe, an gudanar da bikin kaddamar da shirin bidiyo zango na 3 na harshen Tajikistan, mai taken “Bayanan magabata da shugaba Xi Jinping ya fi so”, wanda kafar CMG ta tsara. (Saminu Alhassan)