Bangaren siyasa da kasuwanci na Turai sun nuna adawa da karawa motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin haraji
2024-07-05 14:57:46 CMG Hausa
Bangaren siyasa da kasuwanci na kasashen Turai, sun nuna adawar su ga shawarar da EU ta yanke, ta karawa motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin harajin kwastam. A ganinsu, matakin da EUn ta dauka ya keta moriyar masu sayayya, kuma zai kawo cikas ga yiwa sana’ar samar da motoci a Turai kwaskwarima, kuma hakan zai haifar da mummunan tasiri ga karfin takararsu, kana ba zai ingiza samun daidaito a fannin yawan hayaki mai dumama yanayin da ake fitarwa da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin ba.
A jiya Alhamis ne dai kwamitin EUn ya fitar da wata sanarwa, wadda ke cewa kungiyar ta yi shirin bugawa motoci kirar kasar Sin harajin rangwame da masana’antun kera su suka samu, tun daga yau Juma’a 5 ga watan nan da muke ciki, kamfanonin da aka ware don bincikarsu, za a kara musu harajin kaso 17.4%, da 19.9%, da 37.6%, yayin da sauran kamfanonin za a kara musu harajin kaso 20.8% zuwa 37.6%.
Ministan sufuri na kasar Jamus Volker Wissing, da babban darektan kamfanin BMW Oliver Zipse, da dai sauran shahararrun mutane, sun nuna rashin jin dadinsu ga matakin da kwamitin ya dauka.
Kungiyar ’yan kasuwar Sin dake EU, ta yi kira ga Turai, da ta dawo da hanyar ciniki cikin ’yanci, da gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori a jiya Alhamis, a maimakon amfani da manufar ba da kariya, da kara buga harajin kwastam. (Amina Xu)