An bude taron koli na masana na duniya karo na 8 a birnin Beijing
2024-07-05 13:14:33 CMG Hausa
A jiya ne aka bude taron koli na masana na duniya karo na 8 a nan birnin Beijing. Wakilai sama da 400 daga kasashe da yankuna sama da 20 na duniya sun tattauna manyan kalubalen ci gaban duniya da sauran batutuwa.
Taken taron na bana shi ne "fuskantar rashin tabbas don kyakkyawar makoma ta duniya". Mahalarta taron sun bayyana cewa, a halin yanzu, hatsarori daban-daban da rashin tabbas a duniya na karuwa sosai, kuma ya kamata kasashe su karfafa hadin gwiwar kimiyya da fasaha da hadin gwiwar albarkatun kirkire-kirkire, tare da sa kaimi ga kafa tsarin fasahohin kirkire-kirkire na duniya a bayyane. A matsayinta na wani muhimmin jigon farfado da tattalin arzikin duniya, kasar Sin tana kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya da yin hadin gwiwar kasa da kasa don samun nasara tare. (Yahaya)