Gwamnatin Kamaru ta yi gargadi game ta da rikice-rikice kafin zabe
2024-07-05 11:16:43 CMG Hausa
Ministan kula da yankunan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya bayyana a jiya Alhamis cewa, gwamnatin kasar ba za ta lamunci tayar da hargitsi a kasar kafin zabe ba.
Nji ya shaidawa manema labarai a karshen taron yini biyu da ya samu halarcin gwamnonin yankuna 10 na kasar, domin tattaunawa kan yadda za a gudanar da zabukan da za a yi a shekara mai zuwa cewa, "Ba za a amince da duk wani mataki na kawo cikas a zaben ba, kuma duk wani jagoran siyasa da ya yi yunkurin kawo tsaiko ga zaben zai yi da ya sanin shigar harkar siyasa.”
An dai shirya gudanar da zaben ‘yan majallisu da na kananan hukumomi da na kansiloli a kasar Kamaru a shekara mai zuwa. (Yahaya)