logo

HAUSA

Xi Jinping ya isa Dushanbe don fara ziyarar aiki a kasar Tajikistan

2024-07-05 10:04:38 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan don fara ziyarar aikinsa a kasar bisa gayyatar da takwaransa na kasar Emomali Rahmon ya yi masa a daren jiya Alhamis.

Rahmon ya jagoranci shugaban majalisar dattawa, kana magajin birnin Dushanbe Rustam Emomali da ministan harkokin wajen kasar Sirojiddin Muhriddin da dai sauran manyan jami’ai don tarbar Xi Jinping a filin saukar jirgin sama da wani gaggarumin biki.

Xi Jinping ya isar da kyakkyawar gaisuwa ga gwamnati da jama’ar kasar a cikin jawabin da ya gabatar a filin saukar jirgin sama. A cewarsa, Sin da Tajikistan makwabta ne kuma abokai masu dankon zumunci masu taimakawa juna da goyawa juna baya da hadin gwiwa da cin moriyar da magance kalubaloli tare. Yana fatan tsai da sabbin tsare-tsare tare da Rahmon bisa sabon yanayin da ake ciki wajen raya huldar kasashensu, ta yadda za a hanzarta hadin gwiwarsu a duk fannoni zuwa wani sabon mataki. (Amina Xu)