logo

HAUSA

Kokarin kago kyakkyawar makoma ga matan Sin da Afirka

2024-07-05 16:54:58 CMG Hausa


An yi taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3, mai taken “Ci Gaba na Bai Daya Domin Makoma ta Bai Daya”, a bara a Changsha, hedkwatar lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashen Afrika 53 da na kungiyoyin kasa da kasa da dama. Hu Xiaoqin, magajiyar fasahar gargajiya da ba na kayayyaki ba, wato saka da ciyayin alpine rush ta gundumar Linwu dake birnin Chenzhou na lardin Hunan, kuma shugabar kamfanin fasahar saka ta Xiangfei, daya ce daga cikin masu baje hajoji 32 da suka wakilci Chenzhou yayin baje kolin.

Hu ta ce, “mun samar da kayayyaki masu fasali na musamman domin wannan baje koli, wadanda suka hada da mafici da malafa da zobba da awarwaro da ‘yan kunne. Wadannan kayayyaki sun samu karbuwa a wajen masu baje hajoji da masu ziyara.”

Hu ta halarci baje kolin ne a karo na 3. Ta bayyana cewa, “albarkacin cikar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya shekaru 10, abun alfahari ne a gare ni halartar baje kolin a matsayin wakiliyar mata ‘yan kasuwa daga Chenzhou.”

An fara baje kolin wanda ake yi bayan shekaru 2 ne a shekarar 2019, kuma ya zama wani babban dandali na karfafa dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afrika. A karo na farko, yayin baje kolin, an shirya nune-nunen nasarorin da Sin da Afrika suka samu wajen raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wato BRI da nune-nunen kirkire-kirkire da harkokin kasuwanci na matan Sin da Afrika.

Hu ta ce, “saboda yadda shawarar ke samun karin kuzari a nahiyar Afrika, dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu na kara karfi, tare da shiga wani sabon matakin samun ci gaba mai inganci. Yayin baje kolin, na hadu da wasu tsoffin abokai daga Angola, wadanda suka halarci bikin a matsayin masu baje hajoji. Mun kulla abota ne a lokacin da na gudanar da kasuwanci a Angola, shekaru 10 da suka gabata.”

An baje kusan kayayyakin nau’o’i 1,600 daga kasashen Afrika 29, adadin ya da karu da kaso 166 cikin dari bisa na shekarar 2021. Adadin masu baje hajoji ma ya karu da kaso 70, zuwa 1,500.

Hu ta bayyana cewa, “tawagogin Zambiya da Afrika ta Kudu sun ziyarci Chenzhou bayan baje kolin. Baya ga shawarar BRI, musayar harkokin cinikayya da tattalin arziki tsakanin Chenzhou da kasashen Afrika na ci gaba da karuwa akai-akai, kuma abota tsakanin su, tana kara zurfi.”

Hu ta gabatarwa tawagogin wasu kayayyakin saka da ciyayin alpine rush masu sigogin kasar Sin da ma wasu kayayyaki da suka shafi kirkire kirkire da ci gaban fasahar sakar. Fasahar ta samo asali ne daga wani nau’in ciyawa dake fitowa a kan tsaunukan Linwu. Fasahar saka da ciyayin alpine rush na da dadadden tarihi a Linwu. Sama da shekaru 600 da suka gabata, mazauna suka fara amfani da ciyayin wajen saka tabarmi, inda tabarmin suka yi ta samun karbuwa a hankali.

A shekarar 1954, an gabatar da tabarmin a bikin baje koli na Leipzig da ya gudana a kasar Jamus, inda aka bayyana su a matsayin fasahar hannu ta musamman a duniya. A shekarar 2014 kuma aka sanya fasahar saka da ciyayin alpine rush cikin jerin fasahohin gargajiya da ba na kayayyaki ba da aka yi gado na birnin Chenzhou.

Domin kyautata gado da ma yayata fasahar sakar, a shekarar 2016, Hu ta kafa kamfanin saka na Xiangfei. Ta bayyana cewa, “saboda ruhin kirkire-kirkire, mun samar da na’ika daban daban na kayayyakin saka har 100. Haka kuma muna samar da kayayyaki na musamman ga kwastomominmu. Mu kan saka duk abun da kwastomominmu suke so. Ban da wannan kuma, na tsara wasu shirye-shiryen koyar da dalibai da matasa fasahohin sakar da kuma ba su damar fahimtar fasahar ta gargajiya.”

Hu ta kara da cewa, “kayayyakinmu sun samu asali ne daga halittu, don haka sun dace da kare muhalli, kuma ana sayar da su a gida da kasashen waje. Ina fatan karin Sinawa da baki za su san fasahar gargajiya ta saka da ciyayin alpine rush, kuma karin mutane za su kaunaci kayayyakinmu”.

Hu ta kulla dangantaka da Afrika. Tsakanin 1998 da 2005, ta ziyarci Jamhuriyar Demokradiyyar Sao Tome and Pricipe har sau 2, ta je Guinea-Bissau sau daya, domin koyar da mata fasahohin saka. Ta kuma yi kasuwanci a Angola tsakanin 2005 da 2010.

Yayin ziyararta ta farko a Afrika, ta kasa samun irin ciyayin dake akwai a kasar Sin. Ta kan je tsaunuka a kowacce rana, daga bisani ta samu wasu ganyayyaki da kaba da za ta iya amfani da su wajen koyar da saka.

A wancan lokaci, mata mazauna wurin suna ganin koyon fasahar saka daga kwararriya ‘yar kasar Sin, wani fitaccen shirin koyon sana’ar hannu ne. Yayin da take koyar da saka, Hu ta kulla abota da matan Afrika da dama. Ta kan taimakawa dalibanta idan suka gamu da matsala. Har yanzu bayan ta dawo gida kasar Sin, Hu tana zumunci da wasu daga cikin wadanda ta koyar.

‘Yar Hu ita ma ta shiga kamfanin mahaifiyarta bayan ta kammala karatu daga jami’a. A watan Maris na 2019, Hu da ‘yarta sun je Jamhuriyar Sao Tome and Principe domin ziyartar tsoffin daliban Hu. Hu ta yi farin ciki da ganin cewa har yanzu wadanda ta koyar suna sana’ar saka. Suna samar da kayayyakinsu masu sigar musamman, kuma sun sa kaimi ga ci gaban masana’antun saka da yawon bude ido na yankinsu.

Hu ta koyar da sama da mutane 100 a Afirka, kuma dalibanta su ma sun koyar da nasu dalibai. Hu ta bayyana cewa, “fasahar saka na ba su damar samun kudin shiga da inganta rayuwarsu. Galibin daliban, sun inganta matsayin iyalinsu, kuma sun taimaka wajen samar da ayyukan yi da tabbatar da daidaiton jinsi a Afrika.”

Haka zalika ma, Hu ta ce, “bisa zurfafar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta BRI, ina fatan zan sake zuwa nahiyar Afrika wata rana, domin tattaunawa kan fasahohin saka da abokaina. Ina kuma fatan karin al’ummar Afrika za su samu damar zuwa kasar Sin domin musaya da mu, tare da koyon fasahohin saka.” (Kande Gao)