An yi taron "Inganta AI+ da gina sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko" a Shanghai
2024-07-05 20:18:53 CMG Hausa
Yau Jumma’a, an gudanar da taro mai taken "Inganta AI+ da gina sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko", wanda cibiyar nazari ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami'ar Shanghai Jiao Tong, da dakin gwajin fasahar AI na Shanghai suka dauki nauyin shiryawa a birnin na Shanghai dake kudancin kasar Sin.
A matsayin daya daga cikin ayyukan hukuma, na babban taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil’adama wato AI na duniya na 2024, wannan taron ya hallara wakilai daga bangaren ‘yan kasuwa, da kwararrun masana a fagen ilimin AI, don tattauna wanzuwar AI a matsayin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da raya masana'antu daban-daban. (Safiyah Ma)