logo

HAUSA

Shawarar Sin ta nuna dabarar tinkarar sauye-sauyen yanayin da duniya ke fuskantar

2024-07-05 16:03:47 CMG Hausa

An kira taron koli karo na 24 na majalisar mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da taron koli na SCO+ a Astana fadar mulkin kasar Kazakhstan, inda aka samu sakamako mai armashi dake jawo hankalin mabambantan bangarorin kasa da kasa. SCO ba ma kawai ta nuna kuzarinta ba a kokarin tinkarar sauye-sauye masu sarkakiya da ake fuskanta, har ma ta bayyana iyawarta a fannin taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye tsaro da bunkasuwar duniya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wadannan muhimman taruka biyu, tare da jaddada wajibcin nacewa ga akida mai dacewa da SCO ke bi cikin hadin gwiwa, da kafa wata kungiyar hadin kai mai aminci da juna da tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadata, da sada zumunta, da adalci, gami da daidaito.

Bayan an kammala taron koli na Astana, Sin za ta karbi ragamar shugabancin karba-kaba na SCO din. Sin na fatan hadin kai da sauran mambobin kungiyar don yayata ruhin Shanghai, wanda ya kasance tushen tsarin kungiyar SCO, da ma kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ta kungiyar, ta yadda kungiyar za ta taka rawar gani wajen magance matsalolin da ake fuskanta, a fannin tabbatar da zaman lafiya, da bunkasuwa, da tsaro, da kula da al’amuran kasa da kasa. (Amina Xu)