Xi Jinping ya aike da sakon taya Antonio Costa murnar kama mukamin shugaban kwamitin nahiyar Turai
2024-07-04 14:43:11 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga Antonio Costa, don taya shi hawa karagar shugabancin kwamitin nahiyar Turai.
A cikin sakonsa, Xi ya ce, nahiyar Turai muhimmin bangare ne a cikin madogora da yawa a duniya a ganin kasar Sin. Sin na ba da muhimmanci sosai kan rawar da EU ke takawa a harkokin kasa da kasa. Tana kuma dukufa kan raya huldar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin bangarorin biyu. Ya ce, Sin na daukar huldar bangarorin biyu da muhimmanci, yana mai fatan kara hadin gwiwa da Costa don nacewa ga ka’idar huldarsu wajen zurfafa mu’ammala bisa manyan tsare-tsare, kana da kara fahimtar juna da amincewar juna a siyasance, kazalika da kai ga matsaya daya da habaka hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ta yadda za a tabbatar da bunkasuwar huldar Sin da Turai lami lafiya, da taka rawar gani ga zaman lafiya da bunkasuwar duniya baki daya. (Amina Xu)