logo

HAUSA

Xi Jinping ya halarci taron kwamitin shugabannin mambobin kungiyar SCO ya kuma gabatar da jawabi

2024-07-04 16:11:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta tare da gabatar da jawabi a yayin taron kwamitin shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO dake gudana a Astana, fadar mulkin kasar Kazakhstan a safiyar yau Alhamis.

A cikin jawabinsa, Xi ya bayyana cewa, yawan mambobin kungiyar ya karu zuwa 10 bayan shekaru 23 da kafuwarta, inda kungiyar na shafar kasashe 26 daga nahiyoyi 3, wato mambobi 10 da masu sa ido 2 da abokan tattaunawa 14, matakin da ya inganta tushen hadin gwiwarsu sosai.

Ban da wannan kuma, Xi ya ce, kamata ya yi mu nace ga ra’ayin tsaro na daukar nauyi cikin hadin kai mai dorewa, da tinkarar kalubalolin tsaro masu sarkakiya ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa, da kuma magance tsarin kasa da kasa dake fuskantar kyautatuwa bisa ra’ayin hadin kai da cin moriya tare, kana da kafa wata duniya mai dadadden zaman lafiya, da tsaron duniya gama gari, ya kamata a yi hakuri da juna da hanzarta kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha cikin hadin kai, kana da kiyaye gudanar da tsarin samar da kayayyaki yadda ya kamata, har ma da bullo da karfin bunkasa tattalin arzikin shiyyar. Kazalika, da gaggauta samun bunkasuwa tare, da adawa da shisshigi daga ketare da nacewa ga goyawa juna baya, da mai da hankali ga muradun dake jawo hankalinsu, gami da daidaita bambancin ra’ayi cikin lumana, da warware matsalolin dake kawo cikas ga hadin kansu, kana da dogaro da kai wajen samun bunkasuwar kasa da shiyya.

A yayin taron da aka gudanar a yau, mambobin kunigyar sun kulla yarjejeniyar shigo da Belarus a matsayin mambar kunigyar. (Amina Xu)