logo

HAUSA

Ya zama wajibi Amurka ta sauke nauyin dake wuyan ta game da kasar Afghanistan

2024-07-04 16:04:23 CMG Hausa

Idan ba a manta ba a karshen watan Agustan shekarar 2021 ne dakarun sojin Amurka suka fice daga kasar Afghanistan, bayan shafe shekaru 20 suna yaki a kasar, matakin da ya daidaita kasar tare da barin al’ummun ta cikin mawuyacin hali.

Masharhanta da dama na cewa har gobe, Amurka ba ta sauke nauyin dake wuyanta na tallafawa wajen sake farfado da Afghanistan ba, kuma hakan ya yi daidai da ra’ayin sassan kasa da kasa da suka halarci taro karo na 3 da MDD ta kira game da Afghanistan a birnin Doha na kasar Qatar.

Ko shakka babu, Amurka ba za ta iya sauya halin kunci da ta jefa Afghanistan a ciki ba, duba da irin ta’annatin da ya wakana cikin wadancan shekaru 20, inda yakin da Amurka ta jagoranta ya haifar da kisan ’yan kasar har 174,000, ciki har da fararen hula sama da 30,000, tare da raba kusan kaso daya bisa uku na daukacin al’ummar kasar da matsugunnansu.

Baya ga ainihin abubuwan da suka auku yayin yakin da Amurka ta yi ikirarin ta yi da kungiyar Taliban, yakin ya bar wa Afghanistan kusan kaso 20 bisa dari, na bama-bamai da ba su tashi ba, wadanda ake da matukar bukatar kawar da su, yayin da a lokuta daban daban su kan tashi su hallaka karin fararen hula.

Kazalika, ya zuwa shekarar nan ta 2024, yakin da Amurka ta yi a Afghanistan ya jefa al’ummar kasar da yawansu ya kai kusan miliyan 23.7, adadin da ya haura rabin daukacin ’yan kasar cikin halin bukatar jin kai. Rahotanni sun tabbatar da cewa, a shekarar bana, ana bukatar kashe kudi har dala biliyan 3.06, don tallafawa al’ummun Afghanistan mabukata, wadanda yawansu ya kai miliyan 17.3, ko da yake har zuwa watan Mayun da ya shude, kaso 16.2 bisa dari ne kacal na kudaden aka iya samu domin gudanar da ayyukan.

Tabbas yakin Afghanistan ya dada tabbatar da cewa, tashin hankali ba ya warware wata matsala, illa dai kara ta’azzara halin matsi, da jefa fararen hula cikin halin kunci. Kuma mai yiwuwa tasirinsa ya wanzu zuwa tsawon shekaru masu yawa. Amma yanzu lokaci ne da ya dace Amurka ta saurari muryoyin sassan kasa da kasa, ta sauke nauyin dake wuyanta, na farfado da Afghanistan, ta hanyar kawar mata da takunkumai, da tallafawa wanzar da daidaito, zaman lafiya da ci gaban kasar.(Saminu Alhassan)