logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi kira da a inganta sauye-sauyen dijital a fannin kere-kere

2024-07-04 10:01:54 CMG

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bukaci a yi kokarin inganta sauye-sauye na zamani a bangaren masana’antun kere-kere da kuma kara habaka masana’antun da ke amfani da fasahohi na musamman don samar da sabbin kayayyaki na musamman, a wani yunkuri na zamanantar da tsarin masana’antu.

Li ya bayyana hakan ne a ziyarar aiki da ya kai birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin a ranakun Talata da Laraba. (Yahaya)