logo

HAUSA

Cinikayyar ba da hidimomi tsakanin Sin da sauran sassan kasa da kasa ta karu cikin sauri

2024-07-04 20:54:45 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Mayun bana, sashen cinikayyar bayan da hidimomi tsakanin Sin da sauran sassan duniya ya ci gaba da bunkasa cikin sauri, inda adadin sa ya karu da kaso 16% bisa makamancin lokacin shekarar bara.

Bugu da da kari, bangarorin Sin da na tarayyar Turai EU na tattaunawa, don gane da yunkurin EUn na dora haraji kan ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, inda bangaren Sin ya bayyana fatan tsagin Turai zai kaucewa illar da ka iya shafar hadin gwiwar sassan biyu, da ci gaban masana’antun kirar ababen hawa na Sin da Turai. (Saminu Alhassan)