logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya halarci taron “SCO+”

2024-07-04 19:54:48 CMG Hausa

Da yammacin Alhamis din nan 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kungiyar “SCO+” a birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda kuma ya gabatar da jawabi.

Yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai ko (SCO) na wannan karo, kungiyar ta fitar da Sanarwar bayan taro ta majalissar shugabannin kasashe mambobin ta, da manufar SCO ta ganin kasashe mambobi sun dunkule wuri guda, da ingiza zaman lafiya da adalci a duniya, da zaman jituwa da ci gaba, da kuma sanarwar majalissar shugabannin kasashe mambobin kungiyar, game da bin ka’idar makwaftaka ta gari, da amincewa juna da yin kawance.

Kasar Sin za ta rike ragamar shugabancin kungiyar SCO tun daga shekarar nan ta 2024 har zuwa 2025. Kaza lika, za a gudanar da taron faraministocin kasashe mambobin kungiyar a watan Oktoban bana, a birnin Islamabad na kasar Pakistan. (Saminu Alhassan)