logo

HAUSA

Firaministan Sin ya yi kira da a zage damtse wajen shawo kan ambaliyar ruwa da ayyukan jin kai yayin aukuwar bala’u

2024-07-03 10:47:16 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a zage damtse wajen shawo kan ambaliyar ruwa, da gudanar da ayyukan jin kai yayin aukuwar bala’u yadda ya kamata.

Li Qiang, ya jaddada muhimmancin zama cikin shirin ko ta kwana na tunkarar hadurran da ka iya aukuwa, da karfafa shiri na daidaita kalubalen ambaliyar ruwa, da na ayyukan jin kai yayin aukuwar bala’u, da ceton rayuka, kana da yin aiki tukuru don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, da ma wanzar da daidaiton daukacin harkokin zamantakewar al’umma.

Firaministan Sin, ya yi wannan tsokaci ne lokacin da yake duba ayyukan kandagarkin ambaliya, da na shawo kan matsalar a birnin Jiujiang na lardin Jiangxi, tsakanin ranaikun Litinin da Talata.

Lokacin da ya ziyarci tashar auna tunbatsar ruwa dake mahadar kogin Yangtze da tafkin Poyang, Li ya jaddada muhimmancin hasashen yanayin ruwa, da gaggauta bayar da gargadin aukuwar ibtila’i, yana mai kira da a dora muhimmanci ga aiwatar da matakan karfafa hadin gwiwar sassa daban daban, da kyautata ingancin hasashe.

Har ila yau, Li ya bukaci a kara azamar kyautata aikin kare ingancin ruwa yayin da ake gudanar da ayyukan shawo kan ambaliya, kana a shirya sosai wajen aiwatar da matakai yayin da ake cikin yanayi mai tsanani, da gudanar da ayyukan ceton rayukan jama’a nan da nan, a lokutan da aka fuskanci bala’u.

A daya bangaren, an yi wa firaministan na Sin bayani game da jingar karfafa iyakar kogin Yangtze, da yadda ake lura da kayayyakin aiki na dakile aukuwar ambaliya a kogin.   (Saminu Alhassan)