Shugabannin Sin da Kazakhstan sun yi tattaunawa
2024-07-03 10:21:49 CMG Hausa
Da yammacin jiya Talata ne shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, ya gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping liyafar maraba, inda kuma shugabannin biyu suka gudanar da tattaunawar abota, da sahihiyar musaya dangane da huldar dake tsakanin Sin da Kazakhstan, tare da tattauna wasu batutuwan da ke jawo hankulansu duka. (Saminu Alhassan)