logo

HAUSA

Xi: Sin na goyon bayan shigar Kazakhstan cikin tsarin hadin gwiwar BRICS

2024-07-03 19:19:52 CMG Hausa

A ranar 3 ga wata da rana, agogon Kazakhstan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manema labarai, tare da shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, bayan ganawarsu a Astana, fadar shugaban kasar.

Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan shigar kasar Kazakhstan cikin tsarin hadin gwiwar BRICS, don ta ba da gudummawar da ta dace ga harkokin duniya. Ya ce ya yi imanin cewa, za a samu cikakkiyar nasara a taron kolin Astana da za a gudanar gobe, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zuwa sabon matsayi.

A nasa bangare, Mista Tokayev ya bayyana cewa, ziyarar ta shugaba Xi tana da ma'ana ta musamman ta tarihi, kuma za ta kasance wani sabon mafari na bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen Kazakhstan da Sin zuwa wani matsayi mai girma. (Yahaya)