logo

HAUSA

Sin na maraba da dukkan matakan dake saukaka dangantakar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya

2024-07-03 19:56:28 CMG Hausa

Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da yanayin siyasar Syria. Mao Ning cikin martaninta ta ce, bangaren Sin na maraba da dukkan matakan dake saukaka dangantakar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin.

Game da batun sojojin Amurka dake Syria da suka gudanar da aikin sufurin alkama a Syria, Mao Ning ta bayyana cewa, a gaskiya sun nuna cewa suna a kasar ne, da sunan yaki da ta'addanci, amma a zahiri Amurka tana yunkurin wawushe albarkatu ne, kuma ta kan yi magana kan kiyaye hakkin bil’adama, amma tana keta hakkin rayuwa na al’ummun sauran kasashen duniya.

Game da rahoton cibiyar nazarin tsare-tsare na kasa da kasa ta Amurka da ya ruwaito cewa “Sin na iya kafa tashar sa ido a Cuba”, Mao Ning ta bayyana cewa, babu kamshin gaskiya a rahoton ko kadan. Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Cuba a bude take, kuma babu wani bangare na uku da aka yarda ya yi masa batanci. (Safiyah Ma)